Wannan reshen kamfanin ChinaPower ya shafi kasashe da yankuna 26 dake tsakiya da yammacin Afirka, yayin da aikinsa ya shafi samar da wutar lantarki, da kafa manyan kayayyakin amfanin jama'a, da raya albarkatun ruwa, da kafa kayayyakin jigilar wutar lantarki da sauransu.
An ba da labari cewa, a shekarar 2008, kamfanin PowerChina ya fara aiki a kasar Cote d'Ivoire. Aikin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da ruwa na Soubre da kamfanin PowerChina ya kafa, tasha ce mafi girma a wannan fanni a kasar Cote d'Ivoire, wadda za ta dasa babban tushe na cimma burin kasar na samar da wutar lantarki da yawanta ya kai KW miliyan 4 nan da shekarar 2020.(Fatima)