in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga kwamitin sulhu na majalisar ya yi gaggawar magance tashin hankalin da al'ummar Kasar Sudan ta Kudu ke fuskanta
2016-12-20 09:52:33 cri
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki Moon, ya yi kira ga kwamitin sulhu na majalisar a jiya Litinin, ya dauki matakin magance tashin hankalin da al'ummar Kasar Sudan Ta kudu ke ciki, yayin da al'ummar ke kara tsundunma cikin fargaba.

Yayin bude wani taron kwamitin majalisar dake da wakilcin kasashen goma sha biyar, kan rikicin da ake a kasar Sudan ta Kudu, Ban ki Moon Ya ce lokaci ya yi da ya kamata a rika sanya makomar al'ummar kasar a gaba, maimakon na shugabanninsu.

Ya kara da cewa, tashin hankali a kasar Sudan ta Kudu, barazana ce ga dukkan nahiyar Afrika, a don haka, ya bukaci kwamitin sulhun ya dauki matakin gaggawa na magance rikicin domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

Har ila yau, Ban Ki-moon ya shaidawa kwamitin wani rahoto dake cewa, shugaban kasar Salva Kiir da magoya bayansa, na shirin kai farmaki kan Jam'iyyar adawa ta people's Liberation Movement (SPLM) da kuma rahoton dake cewa, shugaban 'yan adawa Riek Machar da sauran kungiyoyin adawa na neman Karin ayyukan soji.

Ya kuma dora alhakin halin da ake ciki a kasar a kan shugabanninta, ya na mai cewa, baya ga yaudarar jama'a da su ka yi, suna ci gaba da fafutukar ganin sun samu mulki ta kowacce hanya.

Sakatare Janar din wanda ya ce dole ne a hana dukkan bangarori amfani da karfin soji, Ya kuma bayyana damuwa game da yadda ake samun karuwar matsalar kabilanci a kasar, tare da yadda kalamun baatanci ke kara fitowa daga shugabannin.

Ban ki-Moon ya ce har yanzu, shirin wanzar da zaman lafiya a kasar na fuskantar matsala, saboda rashin samun damar isa dukkan sassan kasar, yana mai kira ga gwamnatin kasar ta cika alkawarin da ta dauka na amincewa da tura jami'an wanzar da zaman lafiya.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, tun daga sheakarar 2013 kawo yanzu, dubban Mutane sun rasa rayukansu yayin da sama da miliyan biyu suka rasa matsugunansu sanadiyyar rikicin da ake a kasar. (Fa'iza)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China