in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin sun dawo gida
2016-12-23 20:14:33 cri
Runduna ta biyu ta sojojin kasar Sin masu aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu, ta iso gida bayan shafe watannin 12 jami'an ta na aiki karkashin tawagar MDD. Tawagar dai ta samu yabo na musamman, inda MDD ta ba ta lambar karramawa ta nuna hazaka.

A ranar 8 ga watan Yuli, kofir a rundunar Li Lei dan shekaru 22, da Saja Yang Shupeng mai shekaru 33 suka rasa rayukan su, lokacin da fada ya barke a birnin Juba, tsakanin dakarun gwamnatin kasar karkashin shugaba Salva Kiir, da dakarun 'yan adawa wadanda tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar ke jagoranta.

A cikin wannan wata da muke ciki ne dai tawaga ta 3, ta dakarun na Sin ta isa Sudan ta Kudu domin fara aiki kamar yadda aka tsara.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China