Amurka ce dai ta gabatar da kudurin, inda ta bukaci a sanyawa Sudan ta kudun takunkumin kin sayarwa gwamnatin kasar makamai, da kuma sanya takunkumin kan wasu manyan jiga jigan yan adawar kasar.
Wakilan kasashe 7 ne suka kada kuri'ar amincewa da kudurin, yayi da wakilan 8 suka nuna adawa da kudurin. Hakan dai ya sa kudurin ya gaza samun goyon bayan mambobin kwamitin a kalla 9, inda haka ne kadai zai ba kudurin damar zama doka a kwamitin na MDD.
MDD ta nuna damuwa game da halin tashin hankali da ake fama dashi a Sudan ta kudu, lamarin da ya jefa al'ummar kasar cikin mummunan yanayin neman kai musu dauki, tun bayan barkewar tashin hankalin kasar a shekarar 2013.