in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta kara amincewa da kudurin MDD na kara tura mata sojojin kiyaye zaman lafiya
2016-11-27 13:27:32 cri
A daren ranar 25 ga wata, gwamnatin wucin gadi ta hadin kan al'ummar kasar Sudan ta Kudu ta kara bayyana cewa, ta amince da kudurin da kwamitin sulhun MDD ya zartas game da kara tura mata sojojin kiyaye zaman lafiya a wasu yankunan kasar.

Wani kakakin gwamnatin ya bayyana wa manema labaru cewa, gwamnatin kasar da MDD sun warware dukkan matsalolin da ake fuskanta, kuma gwamnatin din ta amince da kara aika da sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar ba tare da bata lokaci ba.

A ranar 26 ga wata, kwamitin hadin kai na sa ido da kimanta batun Sudan ta Kudu ya bayar da sanarwa cewa, wannan kudurin da gwamnatin Sudan ta Kudu ta tsaida yana da muhimmanci kwarai ga tabbatar da tsaro a Juba, babban birnin kasar, kana kuma ya samar da yanayi mai kyau wajen gudanar da yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudun.

A ranar 12 ga watan Agusta, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri game da tura karin sojojin kiyaye zaman lafiya 4000 a Sudan ta Kudu, inda sojojin MDD dake kasar din zai karu zuwa dubu 17. Ko da yake a ranar 4 ga watan Satumba gwamnatin Sudan ta Kudu ta bayyana cewa, ta karbi wannan kudurin, amma ba a samu ci gaba kan wannan batu ba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China