in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire ta kafa wani tsarin sanya ido na tsaron ruwan tekunta
2016-08-27 12:03:53 cri
Kasar Cote d'Ivoire ta yunkura wajen karfafa tsarinta na sanya ido domin daidaita matsalar rashin tsaro a yankin ruwan tekunta, a cewar wata majiyar tsaro a ranar Jumma'a.

A cewar shugaban ayyukan ruwan tekun Cote d'Ivoire, Kaftan Amara Kone, Cote d'Ivoire ta gudanar da babban kokari domin tsaron yankin ruwan takunta bayan yawaitar ayyukan 'yan fashin teku a shekarun baya bayan nan.

Yankin tekun Guinee dake kunshe da kasashen Ghana, Najeriya, Cote d'Ivoire, Togo da Senegal ya zama wani yankin 'yan gudun hijira ba bisa doka ba, na sumogal din miyagun kwayoyi da makamai, da kamun kifi ba bisa doka ba da kuma lalata muhallin ruwan teku, in ji jami'in.

Haka kuma ya yi maraba da horo da aka yi wa wasu sojojin ruwan Cote d'Ivoire guda dari kan dabarun kama 'yan fashin teku a cikin wadannan shekaru biyu da suka gabata.

Tun lokacin samun jiragen ruwan sintiri guda uku, ruwan Cote d'Ivoire sun samu tsaro. Ana gudanar ayyukan sintiri lokaci zuwa lokaci cikin ruwan tekun, in ji a nasa bangare wani komandan jirgin ruwan sintiri, laftna Ghislain Guie.

Jami'in kuwa ya gamsu da ja da bayan jiragen ruwan 'yan fashin teku a yankin da kuma shaida karfin mayar da martani na jiragen ruwan Cote d'Ivoire. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China