in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Tanzania za ta sauya fadar milki zuwa Dodoma
2016-07-26 10:31:51 cri
Firaministan kasar Tanzania Kassim Majaliwa, ya jaddada cewa, daga watan Satumbar bana ofishinsa zai tashi daga Dar es Salaam zuwa birnin Dodoma.

Gabanin hakan, shugaban kasar John Magufuli ya ayyana cewa gwamnatinsa, za ta sauya fadar mulki daga birnin Dar es Salaam wanda shi ne cibiyar kasuwancin kasar, zuwa Dodoma cibiyar siyasar kasar. Shugaba Magufuli ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, jim kadan baya jam'iyyarsa ta zabe shi a matsayin shugaban ta na kasa.

Shugaban ya ce zai tabbatar da cewa gwamnatin tasa ta kammala komawa sabon matsugunnin nata cikin shekaru 5 na mulkinsa. Magufuli dai zai kammala wa'adin mulkinsa ne a shekara ta 2020. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China