Makamba wanda ya bayyana hakan ga majalisar dokokin kasar da ke birnin Dodoma, ya ce kasar tana hasarar abin da ya kai eka miliyan daya na dazuka a kowace shekara. Yana mai cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata kadai kasar ta rasa yankin da ya kai kwatankwacin fadin kasar Rwanda.
Ministan ya ce, babban abin da ke haddasa wannan matsala ita ce, yadda jama'a ke sare itatuwa domin neman makamashi. Kuma yanzu haka kasar ta fara dandana illar matsalar yanayi, inda ake samun kanfon ruwan sama da karuwar zafi.
Jami'in ya ce, yanzu haka gwamnati ta kaddamar da shirin dasa itatuwa a fadin kasar domin kawar da wannan matsala, inda take sa ran dasa itatuwa miliyan 1.5 a kowace shekara, baya ga samarwa hukumar kare muhalli ta kasar (NEMC) kudi da kayan aiki domin ta yaki duk wasu abubuwan da ke kawo illa ga muhalli. (Ibrahim)