A yayin bikin kaddamar da aikin, Mr. Sun Zhijun, mataimakin shugaban hukumar yada labaru ta kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bayyana cewa, yin hadin gwiwa tsakanin kafofin yada labaru na kasashen Sin da Afirka muhimmin mataki ne dake iya kara fahimtar juna da sada zumunta tsakaninsu. Babban burin shirya wannan aikin neman labaru game da yadda kamfanoni masu jarin Sin suke aiki a Afirka shi ne sanya al'ummomin Sin su kara fahimtar yadda kamfanoni masu jarin Sin suke kokarin gudanar da aikinsu a Afirka, da sakamakon da kasashen Sin da Afirka suka samu bayan sun yi hadin gwiwa. Bugu da kari, al'ummomin kasar Sina ma za su iya kara samun labaru kan yadda kamfanoni masu jarin Sin suke neman ci gaba a kasashen Afirka. Ana fatan karin kamfanonin kasar Sin za su iya zuba jari da kafa sassansu a kasashen Afirka bayan da suka fahimci wadannan labaru, ta yadda za a iya kara karfafa hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya.
Mr. Nape Nnauye, ministan yada labaru, al'adu da wasannin motsa jiki na kasar Tanzania ya bayyana cewa, kafofin yada labaru za su iya yada labaru kan yadda nahiyarmu ta Afirka take samun ci gaba, sannan za su iya taka muhimmiyar rawa wajen kara kusanto al'ummomin Afirka da Sin. (Sanusi Chen)