A wannan rana, firaministan kasar Tanzania Kassim Majaliwa ya ziyarci jihar ta Kagera, don ganewa idonsa barnar da bala'in ya haddasa, inda Kijuu ya ba shi rahoto game da yawan mutanen da suka mutu, da kuma gidajen da suka lalace.
Firaministan ya bayyana cewa, gwamnatin za ta aika da kungiyar kwararru don kimanta hasarar da aka tafka, da nufin ba da taimakon da ya wajaba.
Wani jami'in hukumar sa ido kan girgizar kasa ta kasar Tanzania ya yi kira ga 'yan kasar da su shirya sosai domin tinkarar kananan girgizar kasa da ka iya biyo baya.
A yammacin ranar 10 ga wata ne wata girgizar kasa da karfinta ya kai maki 5.7 a ma'aunin Richter da afkawa kasar ta Tanzaniya. Rahotanni game da labarun girgizar kasa daga yanar gizo ta hukumar binciken labarin kasa ta kasar Amurka, sun nuna cewa, girgizar kasar ta faru ne da karfe 3 da minti 27 na yammancin wannan rana, kuma girgizar kasar bala'in ta fi barna ne a wurin dake da nisan kilomita 44 arewa maso yammacin Bukoba, hedkwatar jihar Kagera, kana zurfin girgizar kasar ya kai kilomita 10.
Kafofin watsa labaru na kasar Tanzania sun bayar da labarai cewa, an ji girgizar kasar a kasashen Ruwanda da Uganda, wadanda ke kusa da jihar Kagera. (Bilkisu)