A yayin bikin budewar taron, jakadan kasar Sin dake Tanzania Lu Youqing ya ce, kasar Sin tana son taimaka wa kasashen Afirka wajen raya harkokin tattalin arziki da zaman takewar al'umma ta hanyoyin samar musu fasahohin neman ci gaba da ta samu.
Haka kuma, ya ce, hadin gwiwar Sin da Tanzania na da makoma mai haske, bayan kasashen biyu suka kulla daftarin hadin gwiwar samar da kayayyaki da makamashi a watan Afrilu na shekarar 2015, sun yi ta tattaunawa kan yadda za a iya inganta hadin gwiwar kasashen biyu a wannan fanni, kuma sun cimma ra'ayi daya kan wasu batutuwan da abin ya shafa.
A nasa bangare kuma, ministan dake kula da harkokin gine-gine, sufuri da kuma sadarwa na kasar Tanzania Makame Mbarawa ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasar Tanzania tana bukatar taimakon kudade, masana da kuma fasahohi matuka, lamarin da ya sa taimakon da kasar Sin ke samar wa kasarsa a wannan lokaci zai taimaka wa kasar Tanzania wajen gaggauta cimma burinta na kasancewar wata kasa mai samun kudin shiga na matsakaicin matsayi. (Maryam)