Tattaunawar neman sulhu na birnin Astana zai taimaka wajen warware rikicin Syria ta hanyar siyasa
Jiya Jumma'a 6 ga wata, manzon musamman na babban magatakardan MDD dake kula da harkokin Syria Staffan de Mistura ya bayyana cewa, tattaunawar neman sulhu kan batun Syria da za a yi a birnin Astana na kasar Kazakhstan, zai karfafa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a baya, sannan, zai samar wa bangarori daban-daban da abun ya shafa, kyakkyawar dama wajen warware sabanin dake tsakaninsu, ta yadda zai taimaka wa kasar ta Syria warware matsalolinta ta hanyar siyasa.
Bugu da kari, ya ce, idan dukkan bangarorin da batun kasar Syria ya shafa da suka hada da gwamnatin kasar, da kungiyoyin adawa da sauran bangarori za su halarci taron neman sulhun da kasashen Rasha da Turkiya suka shirya gudanarwa a ranar 23 ga watan nan da muke ciki a babban birnin kasar Kazakhstan, Astana, wannan zai ba da gagarumin taimako wajen gudanarwar da makamancinsa, da MDD take sa ran gudanarwa a birnin Geneva a ran 8 ga watan Fabrairu mai zuwa. (Maryam)