Jaridar Tehran daily Times ta rawaito gwamnatin Iran tana musanta cewa dakarun Hezbollah na kasar Lebanon za su janye daga kasar Syria.
Jaridar ta ce an jiyo babban mashawarci ga shugaban kotun koli na kasar Ali Akbar Velayati, yana cewa, farfaganda ce kawai da wasu makiya ke yadawa domin yin kafar ungulu ga fafutukar da dakarun ke yi a yankin.
Velayati ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron 'yan jaridu na hadin gwiwa tare da tsohon firaministan Iraqi Nouri al-Maliki wanda ke ziyarar aiki a kasar.
Jami'an kasar ta Iran sun yi tsokaci ne game da martani kan wasu rahotannin kafofin yada labarai dake nuna cewa gwamnatin Tehran ta sauya manufar da ta dauka a baya game da Syria, ciki kuwa har da batun na mayakan Hezbollah, bayan taron mahukuntan bangarorin uku da Rasha da Turkiyya suka yi a Moscow a watan jiya.
A cewar rahoton, jami'an Hezbollah sun nace cewa dole ne mayakan na kasar Lebanon su cigaba da kasancewa a Syria bayan tsakaita bude wuta.
Velayati ya nanata aniyar gwamnatin musulunci ta Iran na cigaba da goyon bayan dakarun fafutuka ciki har da Hezbollah.(Ahmad Fagam)