in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta nemi kwamitin sulhu na MDD ya mara baya ga shirin tsagaita wuta da aka cimma a Syria
2016-12-31 14:10:30 cri

Jakadan kasar Rasha a MDD Vitaly Churkin,ya shaidawa manema labarai a jiya Juma'a cewa, Rasha na fatan kwamitin sulhu na MDD, zai samar da wani kuduri da zai bayyana goyon bayansa ga shirin tsagaita wuta da ta cimma a Syria.

Bayan wata ganawar sirri da kwamitin, Vitaly Churkin ya na fatan a yau Asabar, kwamitin zai kada kuri'ar amincewa da samar da kudurin da zai bayyana goyon bayan MDD ga shirin tsagaita wuta,da kuma na hawa teburin sulhu da bangarori masu rikici a Syria, da zai gudana a Astana babban birnin Kazakhstan.

Shirin tsagaita bude wuta a Syria da Turkiyya da Rasha suka samar, ya kuma samu amincewar gwamnatin Syria da manyan kungiyoyin adawa, ya fara aiki ne da a tsakar daren Alhamis, a wani yunkurin kawo karshen yakin basasa da ka kusan shafe shekaru shida ana yi.

Vitally Churkin ya ce, babu zancen takara tsakanin shirin samar da zaman lafiya na Astana da na Geneva, inda ya ce, ana sa ran MDD ta shiga a dama da ita cikin taron na Astana, idan ya cimma nasara, sai kuma a koma kan na birnin Geneva.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China