Jami'in wanda ya bayyana hakan ga taron manema labarai. Ya kuma bayyana fatan cewa, taron zai taimaka wajen warware rikicin kasar ta Syria. Ya kuma bayyana cewa, MDD tana maraba da duk wani kokari da zai kai ga tsagaita bude wuta da kuma share fagen tattaunawar da za a yi a Geneva a watan Fabrairu.
Staffan de Mistura ya ce ko da a watan da ya gabata, ya yi kokarin shirya taron tattaunawa game da kasar ta Sryia a ranar 8 ga watan Fabrairu,don ganin an kawo karshen rikicin siyasar kasar na kusan shekaru 5, rikicin da alkaluma suka nuna cewa, ya halaka mutane kusan 400,000 a kasar.
Babban mai ba da shawara ga manzon musamman na babban sakataren MDD mai kula da batun Syria Jan Egeland, ya ce kasashen Rasha da Turkiya sun nuna kudirinsu na kai kayan agaji kasar ta Syria da yaki ya wargaza.
Tun a watan Afrilun da ya gabata ne, tattaunawa tsakanin tawagar gwamnatin Syria da dakarun 'yan adawa da ke kokarin ganin bayan shugaba Assad na Syria ta cije, biyo bayan barkewar fada da batun yadda za a shigar da kayan agaji cikin kasar.(Ibrahim)