wata sanarwa ta hadin gwiwa da kungiyoyin suka fitar, ta ce 'yan tawayen za su tsayar da batun tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin kasar da aka shirya yi nan bada jimawa ba Astana babban birnin Kazakhstan.
Sun yi ikirarin cewa, martani suke maidawa ga take dokokin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma kwanaki hudu da suka gabata, karkashin kasashen Rasha da Turkiyya, daga bangaren dakarun gwamnati.
Sanarwar ta ce, bisa kara ta'azarar take ka'idojin, 'yan tawayen sun yanke shawarar tsayar da batun duk wata tattaunawa da ke da alaka da yarjejeniyar Astana, har sai an aiwatar da dukkan kunshin yarjejeniyar tsagaita bude wutar..
Sanawar ta kara da cewa dakarun gwamnati sun ci gaba da kai hari garin Wadi Barada dake arewa maso yammacin Damascus wanda ke karkashin ikon 'yan tawaye, da kuma yankin Rastana dake tsakiyar Lardin Homs.
Sai dai, gwamnati ta ki amincewa harin da take kai wa take ka'idojin yarjejeniyar ne, ta na cewa yaki take da kungiyoyin Nusra Fronta da Is, kuma dukkansu ba sa cikin yarjejeniyar da aka kulla tunda MDD ta ayyanasu a matsayin kungiyoyin 'yan ta'adda.
A cewar Gwamnatin, garin Wadi Barada na karkashin ikon kungiyar Jabhat Fateh Al-Sham da a baya aka san ta a matsayin kungiyar Al-Qaeda mai alaka da Nusra Front, kuma bata cikin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
Yarjejeniyar da aka cimma a baya-bayan nan shi ne irinsa na uku, bayan biyu na baya sun rushe.
An cimma na farkon ne a watan Fabrerun 2016 inda ya yi aiki na tsahon watannin uku kafin ya rushe, yayin da aka cimma na biyun a watan Satumban da ya gabata inda mako daya kawai ya yi kafin ya rushe. ( Fa'iza Mustapha)