Xie Xiaoyan ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da manzon musamman na babban magatakardan MDD dake kula da harkokin Syria Staffan de Mistura a birnin Geneva.
Haka kuma, Mr.Xie ya ce, kasar Sin ta na fatan taron da za a yi a birnin Astana, zai kawo fahimta tsakanin bangarorin da abun ya shafa, tare da kiyaye muradun al'ummominsu yadda ya kamata.
Bugu da kari, ana fatan bangarorin da abin ya shafa za su kulla wata yarjejeniyar da za ta dace da bukatunsu yadda ya kamata.
A ranar 20 ga watan Disamban shekarar 2016 ne, ministocin harkokin wajen kasashen Rasha, Turkiya da kuma Iran suka cimma matsaya kan yadda za a warware matsalar kasar Syria a birnin Moscow na kasar Rasha, inda Rasha ta yi kira da gudanar da taron neman sulhu kan batun Syria a watan nan da muke ciki a birnin Astana na kasar Kazakhstan. (Maryam)