in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka 'yan ta'adda 40 a arewacin Siriya
2017-01-04 11:20:08 cri
Rahotonni daga gidan talabijin na pan-Arab al-Mayadeen TV na kasar Lebanon ya ce, sojojin kawancen kasa da kasa dake karkashin jagorancin Amurka sun yi luguden wuta kan wata matattarar kungiyar dakaru masu tsattsauran ra'ayi mai suna Jabhat Fateh al-Sham dake arewacin kasar Siriya, lamarin da ya hallaka 'yan ta'adda kimanin 40.

Rahoton ya ce, an yi luguden wutan ne a hedikwatar kungiyar dakaru dake jihar Idleb a arewacin Siriya, kuma daga cikin dakarun da aka kashe, akwai jagororin kungiyar da dama. A cewar kungiyar sa ido kan hakkin bil'adama ta Siriya mai hedkwata a birnin London wato SOHR, manyan jagororin kungiyar na gudanar da wani taro a lokacin da aka kai musu harin.

A wata sabuwa kuma, daga ranar 30 ga watan Disambar bara, aka fara aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Siriya wadda kasashen Rasha da Turkiyya suka taimaka wajen daddale ta. Ana gudanar da wannan yarjejeniya yadda ya kamata, ko da yake ana samun musanyar wuta kadan a wasu wuraren kasar. Sai dai sojojin Siriya sun ce, kungiyar IS da kungiyar Jabhat Fateh al-Sham gami da rassanta ba sa cikin kungiyoyin da sojojin gwamnatin Siriya suka tsagaita bude wuta a kansu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China