Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, dorewar kyakkyawar hulda tsakanin kasashen Sin da Amurka, buri ne na bai daya da jama'ar kasashen 2 da ma sauran kasashen duniya ke fatan cimmawa. Mr. Geng ya bayyana hakan ne a yau Jumma'a 6 ga wata a nan birnin Beijing.
Rahotanni na cewa a kwanan baya, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, ya mika wa shugaba Barack Obama na Amurka rahoton cikar wa'adin aikinsa, inda ya ce yanzu haka, huldar da ke tsakanin Amurka da Sin na da matukar muhimmanci ga Amurka a harkokin diplomasiyya. Don haka, ya kamata kasashen 2 su fadada hadin gwiwarsu, yayin da suke daidaita kalubale da dama a duniya. Har wa yau rahoton ya bayyana cewa, har ya zuwa yanzu akwai sabani a tsakanin kasashen 2 a wasu sassa. (Tasallah Yuan)