Jiya Laraba 7 ga wata, an yi babban taron shawarwari kan yaki da masu aikata laifuffuka ta hanyar intanet da dai sauran harkokin da abin ya shafa a tsakanin Sin da Amurka karo na 3 a birnin Washington na kasar Amurka. Wakilin majalisar gudanarwa, kana ministan dake kula da harkokin tsaron jama'a na kasar Sin Guo Shengkun, da ministan shari'a na kasar Amurka Loretta E. Lynch da kuma ministan kula da tsaron cikin gida na kasar Amurka Jeh Johnson sun ba da jagoranci kan taron cikin hadin gwiwa.
Da farko an yi bayani kan sakamakon da aka samu tun da aka fara gudanar da irin wannan taron, inda aka cimma ra'ayi daya kan muhimmancin yin shawarwari kan wannan batu a tsakanin bangarorin biyu, sa'an nan, an cimma ra'ayi daya kan batutuwa da dama wajen zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka domin kiyaye tsaron intanet bisa fannoni daban daban.
A yayin taron, kasar Sin da kasar Amurka sun cimma ra'ayi daya kan harkoki da dama da suka hada da inganta ayyukan yaki da masu aikata laifufuka ta hanyar intanet, yin hadin gwiwa kan kiyaye tsaron intanet, yin amfani da intanet wajen yaki da ta'addanci, samar da labarai ga juna kan harkokin da abin ya shafa da dai sauransu, haka kuma, an cimma sakamako da dama kan wannan aiki bisa jagorancin shugabannin kasashen biyu, kaza kila, bangarorin biyu sun ba da shawara cewa, ya kamata a ci gaba da gudanar da taro karo na hudu mai zuwa a kasar Sin a shekarar 2017. (Maryam)