Hukumar watsa labarun ta bayyana cewa, a yammacin ranar 15 ga wata, wani jirgin ruwan ceto na rundunar sojan Sin ya tarar da wata na'ura a yankin teku na kudu. Domin yin rigakafi kan illar da wannan na'ura za ta kawo wa tsaron zirga zirgar jiragen ruwa da na mutane, jirgin ruwan ceto na Sin ya yi bincike kan wannan na'ura.
Bayan yin nazari a kai ne, daga bisani an tabbatar da cewa, wannan na'urar tafiya a karkashin ruwan teku maras matukin ta Amurka ce, in ji hukumar watsa labarai ta ma'aikatar tsaron kasar Sin, kuma ta kara da cewa, Sin ta dora niyyar mayar da na'urar zuwa Amurka ta hanya mafi dacewa. Sin da Amurka suna mu'amala kan wannan batu lami lafiya.(Fatima)