Yayin tattaunawar tasu, mista Kerry ya jaddada muhimmancin huldar dake tsakanin Sin da Amurka. A cewarsa, tsayawa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, ra'ayi ne na bai daya da jam'iyyu 2 na kasar Amurka suka amince de shi, tuni kuma aka rubuta wannan manufa cikin hadaddiyar sanarwa 3 da aka kulla tsakanin Amurka da kasar Sin.
A nasa bangaren, Wang Yi ya ce, nasarorin da aka samu ta hanyar hadin kan kasashen 2, ba su samu cikin sauki ba, don haka ya kamata dukkanin bangarorin 2 su yi kokarin kare wadannan nasarori, don tabbatar da wanzuwar makomar hulda dake tsakanin kasashen 2.(Bello Wang)