A jiya ne, Donald Trump, shugaban kasar Amurka mai jiran gado ya ce, ya fahimci manufar "kasar Sin daya tak a duniya", amma bai san dalilin da ya sa dole ne Amurka ta amince da manufar ba, illa kasashen Amurka da Sin sun cimma daidaito kan batun ciniki da sauran batutuwa.
Dangane da lamarin, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Litinin cewa, kasar Sin ta kalubalanci sabuwar gwamnatin Amurka da shugaban kasar mai jiran gado da su kara fahimtar yadda batun na Taiwan yake jawo hankali sosai, ta yadda za su ci gaba da bin manufar "kasar Sin daya tak a duniya" da ka'idoji 3 da Sin da Amurka suka amince da su cikin hadin gwiwa, tare da daidaita batutuwan da suka shafi Taiwan, a kokarin magance duk wata matsala ga huldar da ke tsakanin Sin da Amurka. (Tasallah Yuan)