in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwa ita ce hanya daya tak da ta dace Sin da Amurka su bi
2016-12-26 20:05:36 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin da Amurka suna daukar nauyin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da taimakawa ga samun bunkasuwa da wadata a duniya da sauransu, kana suna da moriya iri daya a fannoni da dama. Don haka hadin gwiwa ita ce hanya daya tak da ta dace kasashen biyu su bi.

Rahotanni na cewa, tsohon mai bada taimako ga shugaban kasar Amurka a fannin harkokin tsaron kasa Zbigniew Kazimierz Brzezinski ya bayyana a kwanakin baya cewa, nuna kiyayya ga kasar Sin bai dace da moriyar kasar Amurka ba, kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin shi ne ya fi dacewa. Ko Amurka Ko Sin ba za ta iya jagorantar duniya ita kadai ba, matsayin kasar Amurka a duniya zai dagu ne ta hanyar hadin gwiwa a tsakaninta da Sin.

Game da wannan batu, Hua Chunying ta bayyana cewa, kamata ya yi Sin da Amurka su daina nuna kiyayya da juna, maimakon haka, kamata ya yi su girmama juna da yin hadin gwiwa da samun moriyar juna, da kara yin imani da juna da warware matsalolinsu, da sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakaninsu don amfanawa kasashen biyu da jama'arsu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China