A yayin taron manema labarai na karshen shekarar bana da aka yi a jiya Jumma'a, Mr. Obama ya bayyana cewa, yadda za a kiyaye dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Amurka yana da muhimmin tasiri kan tattalin arzikin duniya da kuma tsaron kasar ta Amurka, shi ya sa, idan dangantakar dake tsakanin kasar Amurka da kasar Sin ta lalace, ko kuma kasashen biyu suka samu sabani bisa dukkan fannoni, babu shakka lamarin zai haddasa illa ga kasashen duniya.
Bugu da kari, Mr.Obama ya ba da shawara ga shugaban kasar mai jiran gado Donald Trump cewa, kafin a yi shawarwari da shugabannin kasa da kasa da kuma na shiyya-shiyya, ya kamata a tabbatar da cewa dukkan ma'aikatan gwamnatinsa su kama ayyukansu yadda ya kamata, sa'an nan su saurari shawarwari da gwamnatocin baya su ba su kan manufofin yadda ake gudanar da harkokin diflomasiyya. (Maryam)