in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar CPPCC ya yi shawarwari da shugaban majalisar dokokin Ghana
2016-04-19 10:44:51 cri
A jiya Litinin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin (CPPCC), Yu Zhengsheng dake ziyara a kasar Ghana, ya yi shawarwari da shugaban majalisar dokokin kasar, Edward Korbly Doe Adjaho a birnin Accra.

A yayin ganawar, Yu Zhengsheng ya bayyana cewa, akwai dankon zumunci tsakanin kasashen Sin da Ghana, tare da samun bunkasuwa. Ana kara samun amincewar juna a fannin siyasa, da yin hakikanin hadin gwiwa tsakaninsu, da yin mu'amala a fannin al'adun gargajiya. Sannan, bangarorin biyu sun yi hadin gwiwa da taimakawa juna a harkokin da suka shafi babbar moriyar kasashen biyu. Hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya na ci gaba da bunkasuwa a yayin da duk duniya ke fama da batun rashin samun bunkasuwar tattalin arziki.

Bayan haka, Yu ya furta cewa, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, an tabbatar da dorewa a fannin siyasa, da raya tattalin arziki, tare da samun babban ci gaba a kasar Ghana. A ganinsa, kasashen Afirka na da babban karfin samun ci gaba, ba shakka za su sami bunkasuwa cikin sauri a nan gaba. A don haka, karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka ya zama wani babban tushe na manufar diplomasiyya da Sin take bi, haka ma manufar da Sin ke tsayawa tsayin daka cikin dogon lokaci.

Dadin dadawa, Yu Zhengsheng ya kara da cewa, shugaban Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Ghana, John Mahama a gun taron kolin Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, inda suka tsara taswirar bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. Kamata ya yi bangarorin biyu su tabbatar da sakamakon da aka samu a lokacin ganawar shugabannin biyu, da zummar sa kaimi ga bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Ghana zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangaren, shugaba Edward Korbly Doe Adjaho ya furta cewa, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, ana ta yin kokarin zurfafa dangantakar abokantaka tsakanin Ghana da Sin, tare da samun babban sakamako wajen yin hadin gwiwa tsakaninsu. Kamata ya yi bangarorin biyu su yi kokari tare, domin sa kaimi ga bunkasa dangantaka tsakaninsu zuwa wani sabon mataki bisa babban tushe da aka dasa. Ghana tana bin manufar 'Kasar Sin daya tak', tana fatan karfafa hakikanin hadin gwiwa tsakaninta da Sin, da kara mu'amala tsakanin jama'ar kasashen biyu, domin sa kaimi ga bunkasa dangantakar dake tsakaninsu, ta yadda za a kawo alheri ga jama'arsu yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China