in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bude kwalejin Conficius na biyu a Ghana
2016-06-03 09:34:42 cri
A jiya ne a hukumance aka bude kwalejin Confocius na biyu a jami'ar Cape Coast a kasar Ghana

Manufar bude kwalejin wanda ake tafiyar da shi tare da hadin gwiwar jami'ar Hunan da ke nan kasar Sin, ita ce koyar da harshen Sinanci da al'adun Sinawa a kasar ta Ghana, bayan da aka kulla yarjejeniya ta fuskar Ilimi tsakanin makarantun kasashen biyu.

Jakadar Sin da ke kasar Ghana Sun Baohong ta bayyana cewa, kasasehn Sin da Ghana sun dade suna amfana da dadaddiyar abokantaka da bunkasuwar hadin gwiwar tattalin arzki, cinikayya,Ilimi da sauran fannoni da ke tsakaninsu.

Ta kuma bayyana cewa, kwalejin Conficius da aka bude a jami'ar Cape Coast, wani sabon ci gaba ne a kokarin da sassan biyu suke yi na kara bunkasa hadin gwiwar da ke tsakaninsu.

Madam Sun ta ce ofishin jakadancin Sin da ke kasar Ghana zai hada kai da bangaren Ghana don ganin kwalejin ya bunkasa yadda ya kamata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China