in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Star Times ya daddale yarjejeniyar hadin gwiwa tare da hukumar wasan kwallon kafa ta Ghana
2016-11-24 13:35:07 cri
Kamfanin mai zaman kansa na kasar Sin na Star Times ya daddale yarjejeniyar hadin gwiwa tare da hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Ghana a jiya Laraba a nan birnin Beijing.

Bisa yarjejeniyar, kamfanin Star Times zai samu iznin tsara shirye-shirye da watsa shirye-shirye game da gasar wasannin kwallon kafa na kasar Ghana a tashar telebijin, da gidan rediyo, da yanar gizo a shekaru 10 masu zuwa. Kamfanin zai kara zuba jari ga tsara shirye-shirye kan gasar wasannin kwallon kafa na Ghana tare da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a fannin wasanni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China