Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, 'yan bindigan sun kaiwa sojojin Nijar da ke gadin sansanin 'yan gudun hijira galibinsu 'yan kasar Mali hari, inda suka kashe a kalla sojoji 22. Majiyar ta ce,ana zaton masu kaifin kishin Islama daga yankin arewacin kasar Mali ne suka kai wannan hari.
Sai dai mahukuntan Nijar ba su ce komai ba game da wannan hari, amma yanzu haka, sojojin Nijar sun baza komarsu don farautar maharan.
Gidan talabijin na kasar Nijar ya ba da rahoto a jiya Alhamis da dare cewa, wasu 'yan bindiga sun kaiwa sansanin 'yan gudun hijira da ke yammacin kasar hari. Yana mai cewa, mutane da dama sun jikkata,amma bai fayyace adadin wadanda suka jikkatan ba.(Ibrahim)