Cikin jawabin da ya gabatar ta gidan talabijin, Mr. Guterres ya ce, hakika babu wanda zai iya cin nasara a yanayi na cikin yake-yake, saboda babu abin da yaki ke haifarwa sai tafka hasara. Kaza lika, ya bayyana cewa, yau ne farkon ranar shekarar 2017, ya kamata mutanen kasa da kasa su yi alkawari tare da shi, wajen mai da zaman lafiya a gaban kome, ya ce, "ya kamata mu mai da zaman lafiya a matsayin babban burinmu, da kuma hanyar da muke bi, sabo da samun zaman lafiya shi ne babban tushen tabbatar da samun girmamawa, fata da kuma ci gaba, ya kamata mu dukufa wajen cimma burinmu na shimfida zaman lafiya a wannan duniyar".
A watan Oktoba na shekarar 2016 ne, aka nada Antonio Guterres a matsayin sabon babban magatakardan MDD na 9 a hukumance, inda aka rantsar da shi a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2016, yayin da ya fara aikinsa kan wannan matsayi tun daga yau ranar 1 ga watan Janairun shekarar bana, wanda wa'adin aikinsa zai kare a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2021. (Maryam)