in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin waje na Sin ya gana da babban darektan ofishin MDD a Geneva
2016-12-12 13:39:17 cri
A jiya Lahadi 11 ga watan nan ne ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da babban darektan ofishin MDD Michael Muller a birnin Geneva.

A yayin ganawarsu, Wang Yi ya bayyana cewa, a matsayin ta na daya daga cikin kasashen da suka kafa MDD, kuma zaunanniyar memba a kwamitin sulhun MDD, kasar Sin ta dade ta nuna goyon baya ga batun hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban da harkokin MDD.

Wang Yi ya ce a yanayin da ake ciki ya dace a kara karfin MDD. Kaza lika a cewar sa Sin na dora muhimmanci, tare da fatan karfafa hadin gwiwa tsakaninta da MDD, domin tabbatar da ra'ayin ta na kawo karshen kalubaloli da matsalolin da duniya ke fuskanta, da kulawa da harkokin duniya baki daya.

An dai yi imanin cewa, tare da bunkasuwarta, Sin za ta kara zuba jari ga harkokin MDD, domin ba da karin gudummawa ga tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasashen duniya baki daya.

A nasa bangare, Michael Muller ya bayyana cewa, yanzu haka rikice-rikice tsakanin kasashen duniya daban daban na kara tsananta, kuma babu wata hanya ta warware wannan matsala, illa hada gwiwa da bangarori daban daban, domin daidaita kalubaloli da matsalolin da duniya ke fuskanta a fannonin zaman lafiya da tsaro da bunkasuwa.

Mr. Muller ya kara da cewa, MDD ta nuna babban yabo ga gudummawar da Sin ke bayarwa a wannan fanni, tare da dora muhimmanci kan babban amfani da tasirin da Sin ta haifar a harkokin duniya. Ya kuma yi fatan MDD za ta karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China