in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira da a kawar da cin hanci don cimma samun bunkasuwa mai dorewa
2016-12-10 13:21:25 cri
Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi jawabi a ranar yaki da cin hanci ta duniya wato 9 ga watan Disambar ko wace shekara, ya bayyana cewa, cin hanci shi ne babban abin da ke kawo cikas ga cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa, ya yi kira ga kasa da kasa da su kawar da cin hanci, da magance shi don gudun kada ya kawo illa ga aiwatar da ajendar samun bunkasuwa mai dorewa ta shekarar 2030.

Ban Ki-moon ya bayyana cewa, kowace kasa tana fuskantar da cin hanci, kana kowace kasa tana da alhakin yaki da cin hanci. Taken ranar yaki da cin hanci na bana shi ne "cin hanci, cikas ne da aka kawowa cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa". Buri na 16 na ajendar samun bunkasuwa mai dorewa ya kalubalanci da kuma rage batutuwan cin hanci da rashawa, tare da kafa hukumomi masu kula da wannan fanni. Yarjejeniyar yaki da cin hanci ta MDD tana taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bangarori daban daban da suke daukar matakan yaki da cin hanci, amma wannan ba zai iya warware matsalar ba.

Ban Ki-moon ya kara da cewa, ya kamata a rike damar ranar yaki da cin hanci ta duniya da jaddada aniyyar kawar da aringizo, da magance cin hanci, don kada ya kawo cikas ga aiwatar da ajendar samun bunkasuwa mai dorewa, da kokarin dukkan mutanen duniya na samun kiwon lafiya da zaman lafiya da wadata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China