A wani bangare na bikin ranar hadin kai da mara baya ga juna ta duniya da ake yi yau, Ban Ki-moon, ya bayyana rashin samar da daidaito da rashin aikin yi da gurbatar muhalli a matsayin muhimman batutuwa ga al'ummomin duniya.
Ya ce a lokacin da ake samun rarrabuwar kawuna a kan batutuwa da dama da suka hada da matsalar kungiyoyin 'yan ta'adda da ta gudun hijra bisa tilas, akwai bukatar mutane su mara baya ga juna wajen cimma muradin da suka sanya gaba, maimakon gujewa juna saboda tsaro.
Ya kuma bukaci kasashen duniya su tabbatar da shigar da al'umma cikin harkokin raya kasa tare da tabbatar da daidaito, ta hanyar aiwaratar da munufofin muradu masu dorewa, da kuma yarjejeniyar yanayi da aka cimma a birnin Paris, da nufin gina ingantacciyar rayuwa ga kowa.
Ana bikin wannan rana ta hadin kai da mara baya ga juna ne a duk 20 ga watan Disamban kowace shekara. Kuma ranar a bana na kira ne da aiwatar da muradun nan goma sha bakwai masu dorewa da nufin yaki da fatara, kare ban kasa, tare da kare mutuncin kowa. (Fa'iza)