in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD zai janye tawaga ta musamman daga Liberiya a shekarar 2018
2016-12-24 13:35:35 cri
A jiya Jumma'a, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kudurin tsawaita wa'adin tawagar kiyaye tsaro ta musamman ta MDD a Liberiya a karo na karshe zuwa ranar 30 ga watan Maris na shekarar 2018, daga bisani za a janye ta daga kasar Liberiya.

A wannan rana, kwamitin sulhu ya zartas da wannan kuduri bisa samun kuri'un amincewa 12 da kuri'un janyewa 3. Bisa kudurin, kafin ranar 30 ga watan Maris na shekarar 2018, kamata ya yi tawagar ta gudanar da aikin kiyaye fararen hula, da taimakawa gwamnatin Liberiya wajen yin kwaskwarima ga hukumomin shari'a da na tsaro da sauransu, tare da nuna goyon baya ga zaben shugaban kasar da na majalisar dokokin kasar a badi bisa bukatun gwamnatin Liberiya.

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD, Wu Haitao ya bayyana a gun taron cewa, a cikin shekaru sama da 10 da take cikin Liberiya, tawagar ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. Sin ta nuna goyon baya ga tawagar da ta ci gaba da kasancewa a Liberiya ta hanya mafi dacewa, domin kara taimakawa kasar wajen tabbatar da zaman lafiya, da kara karfin hukumomin 'yan sanda da na tsaro a Liberiya, domin tabbatar da ganin an gudanar da babban zaben kasar lami lafiya, ta yadda za a bada kariya ga sakamakon da aka samu bayan fuskantar wahalhalu. A sabili da haka, Sin ta jefa kuri'ar amincewa. Wu ya ce, Sin na fatan ci gaba da taka rawar a zo a gani wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun ci gaban Liberiya tare da sauran kasashen duniya baki daya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China