A cikin kudurin, kwamitin sulhun MDD ya yabi Ban Ki-moon, bisa irin kokarin sa a fannin warware rikice-rikice cikin adalci a sassa daban daban na duniya, kana ya yi kira da a yi kwaskwarima kan tsarin kwamitin sulhun MDDr, tare da bada shawarwari ga kyautata tsarin MDDr, da tsarin gudanar da ayyukan ta.
A yayin zaman na jiya, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, kwamitin sulhun yana kokarin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya. Ya ce, a cikin shekaru 10 da ya kwashe yana jagorancin MDD, kwamitin sulhun ya bada izini na kafa tawagogin musamman na kiyaye zaman lafiya, da na siyasa fiye da 10, wadanda suka tinkari yanayi mai sarkakkiya.
Daga nan sai ya yi kira ga kwamitin sulhun da ya ci gaba da kokarin magance faruwar rikice-rikice, da sa kaimi ga warware batutuwan Syria, da na Sudan ta Kudu da dai sauransu.
Ban Ki-moon dan shekaru 72 da haihuwa, ya zama babban sakataren MDD ne a ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2007, zai kuma kammala wa'adin aikin sa a ranar 31 ga wannan wata na Disamba. (Zainab)