Haka kuma, ya ce ana sa ran ceto rayukan fararen hular kasa ta Syria, inda ya ce, tsagaita bude wutar, zai kuma samar da damammaki wajen gudanar da taimakon jin kai a kasar, tare da samar da yanayi mai kyau na gudanar da taron shawarwari kan batutuwan da suka shafi Syria a babban birnin kasar Kazakhstan, Astana.
A dai jiya 29 ga wata ne, rundunar sojan kasar Syria, ta sanar da tsagaita bude wuta a duk fadin kasar, inda kuma sanarwar za ta fara aiki tun daga karfe 12 na daren jiyan.
Sai dai, ba za a dakatar da yaki da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS, da kungiyar Jabhat Fateh al-Sham, da kuma kungiyoyi masu goyon bayansu ba. (Maryam)