Haka zalika, babbar hedkwatar sojojin gwamnatin kasar Syria, ta bayyana nasarar da aka cimma, a matsayin muhimmin ci gaba, a yaki da kasar ke yi da kungiyoyin ta'addanci da kuma magoyon bayansu, tana mai cewa, lamarin ya ba da gagarumin taimako wajen ci gaba da ayyukan kawo karshen ta'addanci a kasar, tare da 'yantar da ita baki daya.
Bugu da kari, rundunar sojojin kasar Syria ta sake yin kira ga dakaru masu adawa da gwamnati da su ajiye makamansu.
Bisa yarjejeniyar janye jiki da aka cimma a baya, an ce, ya kamata dakaru masu adawa da gwamnati su yanje jiki daga birnin Aleppo bi da bi, zuwa yankin karkara dake yammacin birnin da kuma lardin Idlib dake makwataka da shi, haka kuma, dakarun adawar dake lardin Idlib su yarda fararen hula su fita daga garuruwan Kafraya da Foah, wadanda suke karkashin ikonsu. (Maryam)