in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Syria sun ayyana tsagaita bude wuta a fadin kasar
2016-12-29 20:23:31 cri

A yau Alhamis ne sojojin gwamnatin kasar Syria suka ayyana tsagaita bude wuta a dukkan fadin kasar, tun daga tsakar daren gobe Jumma'a agogon kasar.

Wata sanarwa da sojojin suka bayar ta bayyana cewa, tsagaita wutar ba ta shafi dakarun Nusra Front dake da alaka da kungiyar al-Qaida da kungiyar IS ba, kungiyoyin da MDD ta ayyana a matsayin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Shirin tsagaita bude wutar ya zo ne bayan nasarar da sojojin kasar suka samu a fagagen daga masu yawa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China