Yayin babban taron MDD karo na 71, an kada kuri'ar kan daftarin gudanar da binciken wadanda suke da alhakin aikata laifuffukan yaki da sauran miyagun laifuffuka a kasar Syria, inda nan take aka zartas da daftarin bayan an samu kuri'un nuna amincewa guda 105, da 15 na rashin amincewa, yayin da kuma wakilai guda 52 suka janye jiki daga kada kuri'ar baki daya.
Haka kuma, a yayin taron, Mr.Wu ya bayyana cewa, rikice-rikicen da suka auku a kasar Syria sun haddasa babbar matsala ga al'ummomin kasar, lamarin da kasar Sin ta koka da shi, tana mai bukatar bangarorin dake rikicin ya shafa su sake hawan teburin sulhu ba tare da bata lokaci ba, ta yadda za a samu damar tallafawa al'ummomin kasar tare da ba su damar cin gajiyar albarkatunsu yadda ya kamata. (Maryam)