Mevlut Cavusoglu na wannan tsokaci ne bayan wata yarjejeniyar tabbatar da tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Turkiyya da Rasha.
Gidan talabijin na NTV ya ruwaito ministan na cewa, Turkiyya da Rasha sun shirya samar da tsagaita wuta a Syria.
Ministan ya kara da cewa akwai kudure-kudure biyu da aka samar domin warware rikicin, inda ya ce yayin da daya ke mai da hankali wajen tsaigaita wuta, dayan na mai da hankali ne wajen warware rikicn siyasa.
Har ila yau, ministan ya ce shirin tsagaita wutar zai fara aiki a Syria, kowane lokaci daga yanzu. ( Fa'iza Mustapha)