in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana matsayinta game da bukatar ganin kwamitin sulhun MDD ya tattauna batun amfani da makamai masu guba a kasar Syria
2016-12-28 19:07:58 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying ta bayyana a yau Laraba a nan birnin Beijing cewa, Sin ba za ta amince da wani mutum ya yi amfani da makamai masu guba a kowane irin yanayi ba.

Rahotanni na nuna cewa, a kwanakin baya kasashen Birtaniya da Faransa sun tsara wani daftari game da yin amfani da makamai masu guba a kasar Syria. Game da wannan batu, Hua Chunying ta jaddada cewa, wajibi ne dukkan ayyukan kwamitin sulhun MDD game da batun kasar Syria su taimaka wajen warware batun ta hanyar siyasa da kiyaye hadin kai a cikin kwamitin sulhun. A halin da ake ciki a yanzu, kamata ya yi kasashen duniya su kara yin kokarin taka muhimmiyar rawa wajen ganin an warware batun Syria ta hanyar siyasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China