in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudin shiga na kamfanonin intanet na Sin zai kai yuan biliyan 1240 a bana
2016-12-29 10:54:53 cri
Wani hasashe da cibiyar nazarin harkokin sadarwa ta kasar Sin ta fidda, ya nuna cewa, kudin shiga na kamfanonin intanet na kasar Sin, zai kai yuan biliyan 1240 a shekarar bana, zai kuma karu zuwa yuan biliyan 1760 a shekara mai zuwa, wanda hakan ya shaida karuwar kashi 40 bisa dari.

Kana, cikin kamfanonin intanet guda goma da suke kan gaba a kasa da kasa, akwai kamfanoni guda hudu na kasar Sin, watau kamfanonin Alibaba, da Tencent, da Baidu da kuma JD.COM, wadanda suka kasance a matsayi na hudu, da na biyar, da na bakwai da kuma na goma.

A halin yanzu kuma, kamfanonin kasar Sin suna kara zuba jari a kasashen ketare, kamar a kasar Amurka, wadannan kamfanoni suna zuba jari a kamfanonin Airbnb, da Uber da kuma Social Finance da dai sauran manyan kamfanonin kasar. Ban da haka kuma, suna mai da hankali kan zuba jari a kasuwannin kasashen kudu maso gabashin Asiya, da na Latin Amurka, inda za su fara samar da kudade da fasahohin da ake bukata a yankunan. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China