Mutane sama da 1600 wadanda suka zo daga kasashe da yankuna kimanin guda 110 ne suka halarci taron, inda suka saurari jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar ta kafar bidiyo, da kuma jawabin da shugabannin kasa da kasa da na wasu kungiyoyin kasa da kasa suka yi. Haka kuma, an samu sakamako da dama a fannonin yin shawarwari, nuna fasahohin da abin ya shafa, yin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da dai sauransu.
Bugu da kari, a yayin bikin rufe taron, shugaban ofishin sadarwar intanet na kasar Sin Xu Lin ya bayyana cewa, al'ummar duniya suna sa ran inganta mu'amalar dake tsakaninsu ta intanet, kuma za a iya hada mutanen kasa da kasa waje guda ta hanyar yin amfani da intanet. A saboda haka, kamata ya yi gamayyar kasa da kasa su kara mai da hankali wajen daukar matakan da suka dace a fannin kiyaye tsaron intanet. (Maryam)