Yau Alhamis 29 ga wata, ofishin labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fidda takardar bayani game da bunkasuwar harkokin sufuri a kasar, inda aka nuna cewa, cikin shekaru sama da 60 da suka gabata, kasar Sin ta sami saurin bunkasar harkokin sufuri sosai, har tana kan gaba a wasu fannonin da abin ya shafa.
Bugu da kari, gwamnatin kasar Sin ta mai da batun raya harkokin sufuri a matsayin mafi muhimmanci, sabo da babbar gudummawar da aikin ya bayar wajen inganta tattalin arziki da zaman takewar al'umma da dai sauransu.
Haka zalika, cikin takardar, an bayyana cewa, bayan kwaswarimar da aka yi cikin shekaru da dama da suka gabata, ya zuwa yanzu, an cimma nasarori bisa kyautata tsarin kasuwannin sufuri, da tsarin gudanarwar harkokin sufuri, da kuma dokokin da suka danganci sufurin.
Har wa yau, an bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2020, kasar Sin za ta ci gaba da raya harkokin sufuri bisa ka'idojin tallafawa al'ummomin kasar, yayin da za a gaggauta inganta ayyukan sufuri yadda ya kamata.
A karshe dai, an ce, gwamnatin kasar Sin ta dukufa wajen inganta ayyukan sufuri a ko da yaushe, domin raya tattalin arzikinta yadda ya kamata, ta yadda za ta zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya a wannan fanni. (Maryam)