in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana za ta karbi bakuncin bajen kolin farko kan sufurin jigaren saman Afrika
2015-07-02 11:18:03 cri

Gwamnatin kasar Ghana, tare da taimakon cibiyar kasa da kasa kan kwarewa (ICE) ta Abu Dhabi, za ta shirya bajen kolin Africa Air a cikin watan Oktoban shekarar 2016, in ji ministar sufurin kasar Ghana, madam Dzifa Aku Ativor a ranar Talata.

Wannan babban dandali na kwanaki uku zai taimaka wajen gabatar da fitattun jiragen sama, fasahohin zamani da sauran ayyukan da suka jibanci bangaren zirga zirgar jiragen sama, tare da makasudin karfafa masana'antar jiragen sama a Afrika.

Wannan baje kolin, an tsai da da shi da farko a cikin watan Satumban shekarar 2014, amma aka dage shi dalilin annobar Ebola a yankin yammacin Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China