Yawan fasinjojin da suka yi zirga-zirga ta hanyoyin motoci da jiragen kasa da jiragen sama a hutun bikin bazara a kasar Sin ya zarce miliyan 360
An kammala hutun bikin bazara na kasar Sin, yayin da a yanzu haka Sinawa suke komawa bakin aiki daga garuruwansu. Bisa labarin da ma'aikatar sufuri da kamfanin hanyoyin jiragen kasa na kasar Sin, da kuma hukumar jiragen saman kasar suka bayar, an ce, yawan fasinjojin da suka yi zirga-zirga a hutun na kwanaki 7, ta hanyoyin motici, da jiragen kasa, da na jiragen sama a kasar Sin ya zarce miliyan 360.
A hutun na bikin bazara, an yi zirga-zirga ta hanyar motoci a kasar yadda ya kamata, an ce yawan mutanen da suka yi zirga-zirga ta wannan hanya ya kai miliyan 310, adadin da ya karu da kashi 3.2 cikin dari idan an kwatanta da na bara. Kuma yawan mutanen da suka yi zirga-zirga ta hanyar jiragen kasa ya kai kimanin miliyan 45, kuma yawan wadanda suka yi zirga-zirga ta hanyar jiragen sama ya zarce miliyan 8, wanda ya karu da kashi 7.3 cikin dari idan an kwatanta da na bara. (Zainab)