Kungiyar zirga zirgar jiragen sama ta duniya ta yi kira a ranar Talata ga kasashen Afrika da su baiwa bangaren sufurin jiragen sama damar shiga kasuwa, ta yadda wannan bangaren sufuri zai yi takara da kuma gaggauta dunkulewar nahiyar.
Darekta janar na kungiyar zirga zirgar jiragen sama ta duniya (IATA) Tony Tyler ya yi wannan furuci ne a yayin dandalin zirga ziragar jiragen sama a Nairobi, inda ya nuna cewa, ya kamata kamfanonin jiragen saman Afrika su samu 'yancin bunkasa kansu.
Cikin dogon lokaci mai zuwa, wannan zai taimaka wajen gina wani bangaren sufurin jiragen saman Afrika mai karfi da zai iyar fadada reshensa a fadin duniya, in ji mista Tyler.
Ya nuna cewa, Afrika na kan baya ta fuskar yin takara tare da sauran duniya, har ma da kamfanonin jiragen saman Afrika.
Zirga zirga jiragen saman Afrika na da zarafin kasancewa a matsayin wani ginshiki domin bunkasuwar tattalin arziki da ci gaba, in ji mista Tyler, tare da nuna cewa, a cewar wasu alkaluman IATA, bangaren sufurin jiragen sama na tallafawa da kusan miliyan 6,9 na guraben aiki yi a nahiyar Afrika, kuma ya taimaka da kimanin dalar Amurka biliyan 80 na GDP a Afrika.
A shekarar 1999, kasashen Afrika sun rattaba hannu kan sanarwar Yamoussoukro da ke kira ga sassauta harkokin ciniki na bangaren zirga zirga jiragen saman Afrika.
Kasashen mambobin kungiyar tarayyar Afrika sun dauki niyyar aiwatar da yarjejeniyar ta Yamoussoukro kafin karshen shekarar 2017. (Maman Ada)