A jiya ne aka bude bikin baje kolin layin dogo, tashoshin jiragen ruwa da na sama, da kuma matakan tsaro a bangaren tsaron harkokin sufuri a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.
A jawabinsa yayin bikin Samukelo Madlabane, babban manaja a kamfanin Terrapinn da ya shirya bikin na wannan shekara, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kamfanoni da dama ne daga sassa daban-daban na duniya suka baje kolin su a bikin wannan shekara, ciki har da na kasar Sin da Afirka.
Ya ce, bikin wata dama ce ga kamfanonin sufuri na Afirka na yin koyi da juna baya ga musayar kwarewa da sauran dabaru. An kuma yi amfani da wannan biki wajen shirya tarukan karawa juna sani da nufin musayar muhimman bayanai tsakanin mahalarta bikin na bana.
Abubuwan da aka tattauna sun hada da irin damammakin da nahiyar ke da su a bangaren sufuri, hanyoyin samar wa sashen na sufuri kudade, kafofin zuba jari da kuma sabbin fasahohin zamanin da aka samar a bangaren na sufuri. (Ibrahim)