in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta gyara hanyoyin karkara na kilomita dubu dari biyu
2016-02-26 10:06:28 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin sufuri ta kasar Sin Xu Chengguang ya bayyana a jiya Alhamis cewa, a bana, ma'aikatar surufin kasar za ta shirya tare da aiwatar da manyan ayyuka guda 13 domin tallafawa jama'ar kasar yadda ya kamata, haka kuma, biyar daga cikinsu ayyuka ne da ake ci gaba da gudanarwa a shekarar 2015, takwas daga cikinsu su kuma sabbin ayyukan da aka tsara.

Haka kuma, wadannan manyan ayyuka guda 13 sun hada da, gyara hanyoyin karkara na tsawon kilomita dubu dari biyu, shimfida hanyoyin mota a garuruwa dubu 7 dake yankuna masu fama da talauci, kyautata tsarin hanyoyin dake yankunan karkarar kasar, gudanar da aikin kiyaye tsaro da rayuwa a hanyoyi na tsawon kilomita dubu 50, da kuma tsoffin gyara gadoji guda dubu daya da dari biyar da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China