in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin raguwar yankin Hamada a Mongoliya ta gida ya kasance gaba a duk fadin kasar ta Sin
2016-11-07 14:05:39 cri
Bisa binciken da aka yi a karo na biyar dangane da yanayin hamadar jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta, an gano cewa tsakanin shekarar 2004, fadin yankin hamadar ya fara raguwa, kuma cikin shekaru 10 da suka gabata, ana ci gaba da rage fadin yankin a wannan jiha.

Baya ga haka kuma, a tsakanin shekarar 2011 da shekarar 2015, adadin raguwar yankin Hamada da yankin kwararowar ta, ya wuce muraba'in ekta dubu 430, da kuma muraba'in ekta dubu 340, adadin da ya kasance gaba a duk fadin kasar ta Sin.

Haka zalika, ya zuwa karshen shekarar 2015, muraba'in yankin daji a jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta ya wuce muraba'in ekta miliyan 24, adadin da ya kasance mafi girma a duk fadin kasar, wanda kuma ya kai kashi 21.5 bisa dari na duk fadin jihar Mongolia ta gida.

A halin yanzu kuma, jihar ta dasa itatuwa da yawan su ya kai muraba'in ekta 66 cikin ko wace shekara, adadin da ya kai kashi 10 bisa dari na duk fadin kasar a fannin dasa itatuwa, lamarin da ya kyautata muhallin yankin kwarai da gaske. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China